Sanusi Hassan Gambo, wanda tsohon jami'in dan sanda ne da ya yi ritaya, DCL Hausa ta samu labarin cewa dama ya takura wa 'yan ta'addar da ke aiki a wannan yanki na karamar hukumar Kankara.
Majiyar DCL Hausa ta tabbatar da cewa Kwamandan ya fita aiki ne tare da jami'an 'yan sanda na 'mopol' a lokacin da ya cimma lokacinsa. Sai dai had yanzu babu takamaiman halin da su 'yan sandan da suka fita aiki tare suke ciki ya zuwa lokacin hada wannan labari.
Lamarin dai ya faru ne da safiyar Larabar nan a cikin dajin Kankara a lokacin da rahotanni suka nuna cewa sun je kakkabe wasu 'yan ta'adda ne.
A watan Oktobar, 2023 ne Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da jami'an sa kan na Community Watch Corp' su 2,400 domin tallafar jami'an tsaron gwamnati a yaki 'yan ta'adda.