'Yan sanda sun kama masu sana'ar awo da ake zargi da tauye mudu a Gombe 


 Yan sanda sun kama masu sana'ar awo da ke algus a Gombe 


Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a ranar Alhamis ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu Bashir Haruna da Mohammed Isah.


 A cewar wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a na jihar, ASP Sharif Sa’ad ya rabawa manema labarai, an kama wadanda ake zargin ne da laifin hada baki wajen gauraya abinci da ya lalace da mai kyau.


Sa’ad ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da aka ji labarin cewa sun yi algus a buhunan shinkafa 57 inda za su je su sayar wa jama’a da ba su ji ba gani.


Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a karkashin jagorancin CP Hayatu Usman na son sanar da jama’a game da kama yan kasuwar da ake zargi da laifin yin algus da ma fasa-kwaurin abinci, musamman shinkafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp