Ba ku isa ku yi fada da ni ba, martanin Tinubu ga kungiyar NLC
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi Allah wadai da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC ta yi a cikin makon nan.
Shugaba Tinubu ya gargadi 'yan kungiyar ta kwadago da su sani cewa ba NLC kadai ce muryar jama’a ba.
Ya yi magana ne a yayin kaddamar da layin dogo na jirgin kasa na Red Line a jihar Legas wanda ya hada daga Agbado zuwa Oyingbo.