Tinubu ya umurci BUA/Dangote su dawo da tsohon farashin siminti 


 Tinubu ya umurci BUA/Dangote su dawo da tsohon farashin siminti Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci kamfanonin siminti da su koma yadda suke a halin da ake ciki dangane da farashin kayayyaki.


Ministan ayyuka Sanata David Umahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ya ziyarci masana’antar siminti na BUA da ke Sokoto ranar Alhamis.


A cewarsa shugaban ya umurci masana’antun su koma kan tsohon farashin siminti yadda yake a baya.

1 Comments

Previous Post Next Post