Na dauki laifin tsanani da tsadar rayuwa da 'yan kasa ke ciki - Tinubu

 Na dauki laifin tsanani da tsadar rayuwa da 'yan kasa ke ciki - TinubuShugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Nijeriya da su yi hakuri su kuma ci gaba da juriya dangane da halin da matsin da tattalin arzikin kasar ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa akwai haske nan gaba kadan.


Shugaban ya ce yana da cikakkiyar masaniya kuma ya dauki alhakin matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnati.


Ya ce ba zai yi korafi ba amma yana maraba da duk sukar da ake yi masa tunda shi ne ya nemi zama shugaban Nijeriya.


Shugaban ya yi wannan jawabi ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ziyarar da ya kai wa shugaban kungiyar kabilar Yarabawa ta Afenifere a ranar Laraba.

Post a Comment

Previous Post Next Post