'Yan Nijeriya na ci gaba da murnar nasarar da Super Eagles ta samu na doke Angola da ci 1-0


Super Eagles ta doke Angola da ci daya da nema, inda ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Cote d'Ivoire yau Juma'a.

Kwallon wanda Ademola Lookman ya zura a minti na 41 ya baiwa Nijeriya nasara.

An fafata tsakanin kasashen biyu a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny mai daukar mutane 33,000 da ke birnin Abidjan.

Post a Comment

Previous Post Next Post