Mata masu sana'ar Gurasa sun fito kan titunan birnin Kano don nuna damuwarsu da tsadar fulawa, inda suka yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kawo musu dauki.
Shugabar matan masu sana'ar gurasar, Fatima Auwal Chediyar 'Yan gurasa, ta ce kafin yanzu, a da, suna sayen buhun N16,000 amma cikin kasa da wata guda farashin ya tashi zuwa N43,000.
Fatima ta kara da cewa an kori 'ya'yansu daga makaranta domin ba za su iya daukar nauyin karatun su ba da sana’ar da suke da ita ba.