J5 ta yi ajalin wani matashi bayan da kwastam suka biyo ta a Katsina

Wata mota kirar J5 ta yi sanadiyyar mutuwar wani matashi mai suna Mushin Ibrahim mai kimanin shekaru 14 a lokacin da birki ya kwace wa direban motar da yake gudun tsira bayan da jami'an kwastam suka biyo shi.

Lamarin kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, ya faru ne a makarantar firamaren Tudun Wada a Unguwar Tashar Huraira ta karamar hukumar Jibia a jihar Katsina a ranar Asabar din makon jiya.

Wani shaidar gani da ido ya ce jami'an na kwastam na zargin cewa wannan mota kirar J5 ta dauko kayan 'sumoga' ne yayin da suka yi kokarin kama ta.

Bayanai sun ce jami'an kwastam din na karkashin FOU shiyya ta B.

Post a Comment

Previous Post Next Post