'Yan jihar Neja na zanga-zanga kan tsadar rayuwa


'Yan sanda sun harba bindiga don tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Minna na jihar Neja kan tsadar rayuwa.

Da sanyin safiyar Litinin, mata suka datse hanyar Minna-Bidda, inda suke nuna matukar damuwarsu kan yadda farashin kayayyaki ke tashi ba kakkautawa.

Daga bisani, bayan matan sun fito, sai maza ma suka fito suka mara musu baya don ci gaba da zanga-zangar.

Kokarin da 'yan sanda suka yi na shawo kan tarurun jama'ar ya ci tura, har ta kai ga sun harba bindiga a sama.

Post a Comment

Previous Post Next Post