An sake dage shari'ar matashi Sani Zangina da Rarara


Kotun Majistare mai lamba 1 da ke zamanta Lafia babban birnin jihar Nasarawa ta sanar da dage zaman sauraron karar da matashi Alhaji Sani Ahmad Zangina ya kai kan mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara har sai ranar 9 ga wannan wata na Fabrairu.

A zaman kotun da ya gudana a ranar Juma'ar da ta gabata 2 ga watan Fabrairu, da Alkalin kotun....... jagoranta, ya ce hakan ya biyo bayan rokon da lauyan matashi Sani Zangina  ya yi.

Shi dai wannan matashi Sani Ahmad Zangina na neman kotu ta bi masa hakkinsa bisa abin da ya ce tunzura shi da wasu kalaman mawaki Dauda Rarara suka yi a lokacin da ya gudanar da wani taron manema labarai ya yi kalamai kan tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari.

A zaman kotun da aka gudanar a ranar 6 ga watan Janairu da ya gabata, kotun ta dage kai da fata sai mawakin siyasar ya bayyana a gabanta duk kuwa da wakilcin lauyoyinsa da yake samu a duk lokacin da za a gudanar da zaman.

Dama dai sai da kotun ta ba da umurnin a lika wa Mawaki Dauda Kahutu Rarara takardar sammaci a kofar gidansa biyo bayan wahalar samunsa don a hannanta masa wannan takarda.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp