‘Yan majalisar dokokin Najeriya 60 sun kada kuri’a
kan bukatar sauya tsarin tafiyar da gwamnatin Najeriya zuwa tsarin gwamnatin
Prime minister a maimakon shugaban kasa wanda aka fara amfani da shi a
jamhuriya ta farko.
‘Yan mahalisar su 60
sun gabatrwa majalisar wani kwarya-kwaryan kundin tsarin mulki, wanda suke
ganin matukar aka bi shi, za’a yi nasarar mayar da kasar kan tsarin na Prime
minister nan da shekara ta 2031.
Da yake yiwa manema labaran fadar shugaban kasa
jawabi bayan gabatar da kundin, mai magana da yawun yan majalisar su 60
Abdulsamad Dasuki, ya ce lokaci yayi da ya kamata a kawo karshen tsarin
shugaban kasa mai cikakken iko a Najeriya, la’akari da tsadar da yake da shi.
Duk da dai ‘yan majalisar sun nuna shakku game da
samun nasarar sauya tsarin gwamnatin kasar nan da shekara ta 2031, amma sun ce
karfin da tsarin shugaban kasa mai cikakken iko ya baiwa shugaban kasar ya yi
yawan da yake janyo ci baya ga kasa.