Mun gaji da ba talakawa hakuri, don suna gab da yi wa gwamnati tawaye - Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya gargadi gwamnatin Najeriya ta gaggauta daukar matakin saukaka wa talakawa rayuwa da fatattakar yunwa, matukar ba haka ba kuma ta kuka da kanta kan matakin da talakawan zasu dauka akanta.

Da ya ke yiwa manema labarai jawabi a Arewa House da ke jihar Kaduna Sarkin musulmin yace sarakunan gargajiya dana shugabannin addini sun gaji da tausar talakawa da kuma basu hakuri, don haka babu makawa illa gwamnati dauki matakin saukaka rayuwa.

Ya ce a yanzu talakawa sun kai geji kuma tura ta kai bango kana sarakunan gargajiya ba zasu iya tare talakawa ba  idan suka fusata da gwamnati.

Ya ce kullum maganar kenan da gwamnati ke yi musu kan suci gaba da tausar talakawa, har zuwa yaushe ne za’a ci gaba da bada hakuri? Har zuwa yaushe ne talakawa zasu ci gaba da mutuwa da yunwa da sunan hakuri? a yanzu lokaci ne da gwamnati zata yi hakuri ta dauki matakin da ya dace.

“Mun jima muna rokon talakawa, a yanzu mun gaji, kunyar su muke ji, sun fara daina yarda da maganar mu, don babu wata alamar sauki daga gwamnati don haka matukar gwamnati bata dawo cikin hayyacin ta ba, to duk matakin da talakawa suka dauka tabbas ta kuka da kanta” inji sarki musulmi.

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp