Kayan abinci sun yi sauki a wasu sassan arewacin Nijeriya

To a wannan makon dai Masara ta fi sauki a yankin Arewacin Nijeriya sama da kudanci, inda a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano aka sayar da buhun Masara mai cin kwano 40, kan kudi N57,000, haka batun ya ke a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, yayin da a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, farashin buhun ya kama N60,000, daidai.

A makon nan dai, an sayar da buhun Masarar a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kan kudi N62,000-65,000 Amma a kasuwar Song na jihar kuwa aka sayar da Masarar N58,000. Sai dai fa batun ya sha bamban a kasuwar Gwalantabal da ke yankin karamar Hukumar Song duk a jihar Adamawa, inda farashin Masarar ya kama N53,500, amma a kasuwar Monday Market, Maduguri, jihar Borno farashin buhun Masarar ya kama N55,000.

Bisa ga dukkan alamu dai, ana ci gaba da samun sauki a yankin arewacin kasar nan, inda aka sayi buhun Masarar a wannan makon kan kudi N42,000 a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko, a jihar Gombe.




To Idan muka leka kasuwar Giwa a jihar Kaduna Buhun Masarar ya kama N51,000 a wannan makon.

Ta bangaren shinkafar gida kuwa, babban buhu an sai da shi kan kudi N120,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna, kasuwar Mai'adua jihar Katsina kuma farashin buhun Shinkafar ya kama N115,000, a kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuma kudin shinkafar Hausar ya kama N110,000. Sannan akwai kasuwar Monday Market Maduguri, jihar Borno da aka sayar da shinkafar Hausa N108,000.

A kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuma, an sayar da buhun shanshera na shinkafar mai L N40,000 -43,000. A kasuwar Kashere ta jihar Gombe ma dai batun bai sauya zani ba, kudin N40,000-43,000.

Ita kuwa shinkafar waje ta fi sauki a kasuwar Monday Market, Maduguri a jihar Borno, inda ake sayar wa kan kudi N60,000. Sai dai an samu 'yar tazarar N5,000, tsakanin jihohin Adamawa da Borno, yayin da a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawar ake sayar da shinkafar N65,000, sai kuma kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kudin buhun shinkafar ya kama N70,000 ita ma dai Kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuɗin shinkafar bature N70,000 ne a wannan makon.

A ɓangaren taliyar Spaghetti kuma N12,500 ne a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, ita ma dai kasuwar Monday Market, Maiduguri a jihar Borno haka zancen ya ke, sai kasuwar Kashere da ke jihar Gombe N12,700, a kasuwar Mile 12 International Market Lagos farashin kwalin taliyar ya kama N14,000, sai kasuwar Giwa jihar Kaduna kuma kuɗin Spaghetti 'yar Waje N18,000 daidai.




3 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp