Wata kotun shari'ar Musulunci da ke zamanta a GRA, Zaria jihar Kaduna ta umurci da Hon Sani Sha'aban dan takarar Gwamna a jihar karkashin jam'iyyar ADP a zaben da ya gabata da ya biya bashin Naira milyan 11.2 da wani Alhaji Umar Faruq Abdullahi ke binsa.
Alkalin kotun Alhaji Ishaq Madahu da ya ya ke hukuncin, ya kuma umurci da a kwace kadarar Hon Sani Sha'aban da ya ba da ita a kafin a bashi wancan bashin.
Kazalika, kotun ta umurci da a gaggauta neman wanda zai sayi wannan kadara, domin a biya wannan bashi da ake bin Hon Sani Sha'aban, har kotun ta ce idan kudin wannan kadarar ya zarta kudin bashin da ake binsa, za a maido masa da sauran.
Haka kuma kotun ta umurci Hon Sani da ya yo ciko muddin wannan kadarar ba ta kai yawan kudin da ake binsa ba.
Idan za a tuna dai, an sa hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Hon Sani Mahmud Sha'aban (Dan Duran Zazzau) da Alhaji Umar Faruq Abdullahi don fitar da shi (Hon Sha'aban) daga wata matsala a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE a shekarar 2018.