Gwamnan Katsina Dikko Radda ya kafa dokar hana boye kayan abinci a jihar


Gwamnan Katsina Dikko Radda ya kafa dokar hana boye kayan abinci a jihar


Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya saka hannu kan dokar da za ta hana mutane boye kayan abinci.


Kafa wannan doka na nufin hana wasu 'yan kasuwa da ake zargi da boye kayan abinci a rumbuna daban-daban don kayan abincin su yi tsada.


Kazalika Gwamnan ya kafa wani kwamiti na musamman da za a dora wa alhakin bi lungu da sako na jihar don zakulo mutanen da suke boye kayan abinci.


Dokar ta haramta duk wani yunkuri na boye kayan abinci a duk fadin jihar. Kazalika, dokar ta lissafta kayan abinci da suka hada da shinkafa, masara, gero, dawa, waken suya, gyada da ma duk wani nau'in kayan abincin da karancinsa zai jefa al'ummar jihar Katsina cikin halin ha'ula'i.


Bugu da kari, wannan doka ta fayyace karara cewa duk mutumi ko kamfanin da aka samu da laifin boye kayan masarufi, to ya saba dokar da za a iya hukunta shi karkashin sashe na 114 a kundin penal code.


Sannan hatta wurin da aka kama cewa ana boye wadannan kayan abinci, za a barke shi a fitar da abincin don sayar wa al'umma a farashin da ya dace.


Ta bangaren kwamitin karta-kwana na task force da Gwamnan ya kafa kan wannan batu kuwa, an dora masa alhakin zakulo masu boye kayan masarufin a cikin jihar.


Bugu da kari, an kwamitin zai hada da jami'an tsaro don su kamo tare da gurfanar da wadanda aka samu da laifin. Kazalika, kwamitin zai gana da masu ruwa da tsaki kan harkar kayan masarufi a jihar don gudun kitso da kwarkwata.


Sannan wannan kwamitin zai rika kula da yadda ake safarar kayan abincin, daga sassan jihar daban-daban da ma tsallakawa da shi kasashen waje.


Ana kyautata zaton kwamitin zai kunshi shugaba da karin mambobi 10 da za su gudanar da wannan aiki.


Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD ya rarraba hannu kan wannan doka a ranar Juma'ar nan 16 ga watan Fabrairun, 2024.


Isah Miqdad

SSA Digital Media for Chief Press Secretary 

16/2/2024

Post a Comment

Previous Post Next Post