Gwamnatin Najeriya ta sanya Interpol cikin masu bincike kan kwaikwayar sa hannun shugaba Buhari

 


Gwamnatin Najeriya ta bukaci ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol su sanya wasu mutane uku cikin jerin wadanda suke nema ruwa a jallo sakamakon zargin su da hada baki wajen kwaiwakayar sa hannun tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, inda suka fitar da dala miliyan 6 da dubu dari 230 daga asusun kasar.


Mutanen da ake zargi sun hadar da Adamu Abubakar da Imam Abubakar da kuma Odoh Eric Ocheme.

Tuni dai gwamnatin kasar ta shigar da karar mutanen uku, kan zargin satar bayanan tsohon shugaban kasa, yiwa kasa zagon kasa da yaudarar ma’aikatan gwamnati.

Tun farko mutanen sun rubuta takarardar bayar da umarnin fitar da wadannan kudi daga asusun gwamnati dauke da sa hannun shugaba Buhari, sannan suka kaiwa sakataren gwamnati na wancan lokaci Boss Mustapha wanda ya fitar da kudin, karkashin babban bankin kasar.

Bayanai sun ce an yi amfani da kudaden ne wajen raba su ga kungiyoyin da ke sanya idanu kan zaben da aka gudanar a kasa.

 


Post a Comment

Previous Post Next Post