An kwaikwayi sa-hannun Buhari wajen fitar da kudi dala miliyan 6.2 - Boss Mustapha

 

An kwaikwayi sa-hannun Buhari wajen fitar da kudi dala miliyan 6.2 - Boss Mustapha

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya musanta bayanan da ce cewa gwamnatin da da shude ta amince an fitar da dala miliyan 6.2 da ake zargin an yi amfani da su wajen warewa masu sa ido na kasa da kasa a zaben kasar.

Mustapha wanda ke ba da shaida a ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce an yi amfani da sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na bogi.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da kara da aka yi wa kwaskwarima masu dauke da tuhume-tuhume kusan guda 20.


Post a Comment

Previous Post Next Post