An kwaikwayi sa-hannun Buhari wajen fitar da kudi dala miliyan 6.2 - Boss Mustapha


Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha,  ya bayyana cewa an kwaikwayi sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, don ba da izinin cire tsabar kudi dala miliyan 6.2 daga asusun babban bankin Najeriya.

Mustapha wanda ke ba da shaida a ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja a yau Talata, yace sa hannun tsohon shugaban kasar na jabu ne ba na gaskeba.

Da yake bayanin abin da ya faru, Mustapha ya ce shi ko tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su amince da a cire kudaden ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp