Tsadar rayuwa: Gwamnatin tarayya zata kafa hukumar daidaita farashin kayan abinci


Gwamnatin Tarayya na shirin kafa Hukumar da zata kula da daidaiton tashin farashin kayan masarufi a kasar

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yau Talata a wajen wani babban taro na kwanaki biyu kan sauyin yanayi da tsarin abinci a Abuja.

Shettima ya ce za'a baiwa hukumar damar tantancewa da daidaita farashin kayan abinci, tare da kula da tsarin tanadin abinci don daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci.

Post a Comment

Previous Post Next Post