Tinubu ya gwangwaje yan wasan Super Eagles da gidaje da filaye a Abuja


Shugaba Tinubu ya gana da kungiyar kwallon Super Eagles, inda ya karrama su da lambar yabo ta kasa MON da gidaje a babban birnin tarayya Abuja da filaye ga kowannen su a yau Talata.

Tawagar ta samu jagorancin ministan raya wasanni, Sanata John Owan Enoh gami da jami'an hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafan dai ta zo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala a ƙasar Cote d’Ivoire.

Post a Comment

Previous Post Next Post