Nijar: Janar Tiani ya yi wa gwamnatinsa garanbawul
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar Janar ABDOURAHAMANE Tiana ya yi wa gwamnatin sa kwarya kwaryar garan bawul
Sakataren gwamnatin kasar ya bayyana hakan ta kafar talabejin din kasar
Kuma wannan garan bawul ya shafi ma'aikatu uku ne da suka hada da ta ma'adanai, ta man fetur da ta makamashi inda aka nada musu sabbin ministoci