'Yan bindiga sun kai mummunan hari kusa da sansanin sojoji a Katsina

Wasu 'yan ta'adda da har zuwa lokacin hada wannan labari ba a tabbatar da adadinsu ba, sun hallaka wani mutum ta hanyar kone shi da ransa a kauyen 'Yar Nasarawa da ke cikin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Majiyar DCL Hausa a yankin, ta tabbatar da cewa maharan sun shiga kauyen ne da daren Litinin wayewar Talatar nan, inda a jimilce suka kashe mutane 8.

Kazalika, 'yan ta'addar, an rawaito cewa sun kuma kona shaguna akalla 6, da rumbunan hatsi 7 da gidaje akalla 6 da motoci da baburan da har yanzu ba a kai ga tantance ko nawa bane.

Bugu da kari, a yayin harin, bayanai sun zo wa DCL Hausa cewa an raunata mutane da dama sannan 'yan ta'addar sun kwashi mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba.

Sai dai, a kauyen Maigora, daya daga cikin mazabu a karamar hukumar ta Faskari, nan ma wasu maharan ne suka yi dirar mikiya, suka yi awon-gana da dabbobin da ba a san adadinsu ba ya zuwa yanzu.

Haka kuma, duk a daren na Litinin wayewar Talatar nan, wasu maharan sun kutsa kai kauyen Ruwan Godiya duk a karamar hukumar ta Faskari, inda suka yi ayyukan ta'addancin da har ya zuwa lokacin hada wannan labarin ba a kammala tantance yawan barnar da suka yi ba.

Kauyen 'Yar Nasarawa dai bai fi nisan kilomita 5 ba zuwa babbar hedikwatar karamar hukumar Faskari. Sannan a kusa da su akwai sansanin nan na sojoji da ake kira da 'Army Super Camp, Faskari' da aka bude tun zamanin Lt. Gen Turkur Yusuf Buratai na babban hafsan sojin Nijeriya.

Karamar hukumar Faskari, na iyaka da jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post