'Yan sanda sun tabbatar da mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Katsina


Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kai hari a kauyen 'Yar Nasarawa a karamar hukumar Faskari ta jihar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya aike wa DCL Hausa, ta ce 'yan bindigar sun kashe mutane 6, sun kuma raunata 10.

Kazalika, sanarwar ta ce 'yan bindigar sun kone gidaje 3 da motoci kusan 10. Tuni dai jami'an tsaro sun kewaye yankin a yunkurin kama wadanda suka yi wannan aika-aika.

Da sanyin safiyar Talatar nan, DCL Hausa ta ba da labarin cewa wasu 'yan ta'adda sun farmaki kauyen 'Yar Nasarawa a karamar hukumar Faskari, inda har suka kone wani mutum da ransa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp