Nagartattun Finafinan mu ka iya dawo da martabar Nijeriya.


Shugaban Hukumar kula da harkar shirya Finafinai a Najeriya kuma jarumi a Kamfanin shirya finafinai na Kannywood Ali Nuhu yana mai hangen cewa shirya nagartattun finafinai ka iya dawo da martabar Najeriya a idon Duniya.

Ali Nuhu ya gano wata matsala da ya ke gani idan aka shawo kanta, nagartattun finafinai na ƙasar zasu iya kaiwa kaso saba'in zuwa saba'in da biyar cikin ɗari, saɓanin yanzu da ake da kaso talatin zuwa talatin da biyar cikin ɗari na nagartattun finafinai a ƙasar.

Daga cikin turbar cimma wannan buri na sabunta Najeriya ta hanyar finafinai Ali Nuhu a wani labari da Jaridar Daily Trust ta wallafa ya ce akwai karin ilimi ga masu harkar ta film da kuma samar musu kayakin aiki irin na zamani.

A cewar Ali Nuhu akwai wasu da ke ɓata suna Najeriya daga cikin 'yan ƙasar wadda idan aka dukufa ta hanyar nan ta finafinai za'a wanke ƙasar da waccan ɓãtanci, ya kuma nuna muhimmancin manyan kamfanonin finafinai na Kannywood da Nollywood su hada kai wuri guda.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp