An rubuta wa majalisar dokokin Kano wasikar neman a rusa masarautu 4, a dawo da guda daya
Wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” (The Kano Electorate), ta rubuta wa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman a sake duba dokar kafa karin masarautu hudu na Gaya, Rano, Karaye da Bichi da gwamnatin Ganduje ta yi.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga Fabrairu, 2024 da aka aika wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano ta nemi a rusa masarautun tare da maido da Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, inda kungiyar ra ce hakan zai samar da hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da kuma makwabtanta a cewar wasikar.
A ranar 5 ga watan Disamba, Shekarar 2019, tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya rattaba hannu kan dokar masarautu kuma a nan take majalisar dokokin ta amince da dokar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa ana ta cece-kuce kan shirin mayar da Sarki Muhammadu Sunusi ll, kan karagar mulki tare da rusa sauran. masarautun wadanda ake tunanin an kirkire su ne domin tozarta tsohon Sarkin.