Kotu ta umurci Tinubu da ya karya farashin kayan masarufi
Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Legas, ta umarci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta daidaita farashin kayayyaki da na man fetur, a cikin kwanaki bakwai.
Alƙalin Kotun Mai shari'a Ambrose Lewis-Allagoa, shine ya bada umarnin a yayin zaman kotun, bayan da Lauyan nan mai fafutuka, Mista Femi Falana (SAN) yayi Ƙarar Gwamnatin kan hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Falana ya shigar da ƙarar ne, inda ya dogara da sashe na 4 na dokar kayyade farashin kayayyaki, kuma tuni kotun ta umarci gwamnati da ta gyara farashin kayayyakin.
Kayan da umarnin ya shafa sun haɗar da madara, gari, gishiri, sukari, kekuna, ashana, babura, motoci, man fetur, gas da kuma kalanzir.
Kuma dai Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne ga Ministan shari'a na Nijeriya da kuma Hukumar Kula da Farashi Kaya ta ƙasar (PCB).