Jam'iyyar APC ta yi gargadi kan rusa masarautun Kano.
Jam’iyyar adawa ta APC ta gargadi gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya yi taka-tsan-tsan don gudun kada a tura shi yin wani abu da zai iya shafar zaman lafiya da ake samu a jihar Kano.
Jam’iyyar APC ta yi gargadin cewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga tsarin masarautun, kamar yadda Ganduje ya kirkiro, na iya tayar da zaune tsaye a garin muddin suka dauki matakin hakan kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
A ranar 5 ga watan Fabrairu ne wata kungiya mai suna‘Yan Dangwalen Jihar Kano ta rubutawa Majalisar Dokokin Jihar Kano, takardar neman a sake duba dokar kafa karin masarautu hudu a Gaya, Rano, Karaye, da Bichi da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi.
Kungiyar ta kuma yi kira da a mayar da tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II.