Gwamnatin Kano za ta fara farautar 'yan kasuwa da ke boye kayan Abinci

 Da Dumi-Dumi: Hukumar PCACC a Kano ta fara farautar 'yan kasuwa da ke boye kayan Abinci. 


Hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta ce ta fara aikin leken asiri domin farautar ’yan kasuwa da ke taskance kayan masarufi da nufin magance hauhawar farashin kayayyaki a jihar.

Shugaban Hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis.


Muhyi ya ce hukumar ta PCACC na fuskantar matsananciyar matsin lamba wajen matakin da ta dauka kan irin wadannan ‘yan kasuwa saboda irin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post