Kungiyar kwadago ta NLC ta fitar da sanarwar yajin aiki nan da mako biyu.

 Kungiyar kwadago ta NLC ta fitar da sanarwar yajin aiki nan da mako biyu. 


Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun fitar da sanarwar tsunduma yajin aiki nan da kwanaki 14 masu zuwa muddin gwamnatin tarayya ba ta yi abin da ya dace game da tsadar rayuwa da 'yan kasa ke ciki.


Sanarwar ta kuma ce kungiyoyin sun yanke wannan shawarar ne saboda gazawar gwamnatin Bola Tinubu na aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ranar 2 ga Oktoba, 2023, biyo bayan cire tallafin da aka yi wa man fetur.


Shugabannin NLC da TUC sun bayyana bakin cikinsu cewa duk da kokarin da kungiyoyin kwadago ke yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma'aikatan gwamnati, da alama ita gwamnatin ba ta damu da dimbin wahalhalun da ake fama da su a fadin kasar ba.


Wadannan tsare-tsare guda biyu, kamar yadda suka yi hasashe, ya yi wa tattalin arziki mummunar illar ga talakawa da ma’aikatan Nijeriya.

1 Comments

  1. Shugaban kasa bola Ahmed tinubu Ya temaka mu na don Allah muna cikin tsadar rayuwa kasan mu ta Nigeria

    ReplyDelete
Previous Post Next Post