An kashe jami'an sa kai na 'Community Watch Corp' a Katsina


Wasu bayanai da DCL Hausa ta tattara sun ce an kashe jami'an sa kai na 'Community Watch Corp'da ke aikin taimakawa a samar da tsaro a jihar Katsina su biyu a kauyen Mai Dabino na karamar hukumar Danmusa ta jihar.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce 'yan ta'adda ne suka kai wani samame da sanyin safiyar Juma'ar nan a kauyen na Mai Dabino, inda aka yi ta dauki-ba-dadi tsakaninsu da jami'an sa kan, har suka yi nasarar hallaka biyu daga ciki.

An dai yi jana'izar daya tun da misalin karfe 7 na safe, a yayin da shi ma dayan ya rasu bayan harbin bindiga da ya samu da misalin karfe 11 na safiyar nan.

Majiyar ya ce yanzu haka yankin nasu na Mai Dabino saura jami'an sa kan Community Watch Corp' 16, cikin 19 da gare su. Dama dai an kashe daya ranar wata Juma'a a lokacin da suke kan hanyar raka su zuwa kasuwar 'Yantumaki, sai gashi yau ma an kashe karin biyu.

An dai yi arangamar a bakin garin na Mai Dabino inda jami'an sa kan da sauran al'ummar gari suka fita don kare kansu a lokacin da suka ji duriyar 'yan ta'addar na zuwa kauyen nasu.

Majiyar DCL Hausa ta ce yanzu haka kasuwar 'Yantumaki da suka saba zuwa duk mako a ranar Juma'a ta gagare su, kasancewar sojojin da ke raka su, sun rasa motarsu daya cikin motoci biyun da suke amfani da su wajen rakiyarsu zuwa kasuwar.

Ya zuwa lokacin hada wannan labarin dai babu cikakken bayanin ko 'yan sa kan sun yi nasarar hallaka wasu daga cikin 'yan ta'addar da suka kai musu wannan samame.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta hannun kakakinta ASP Sadiq Abubakar Aliyu ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce dan banga na Vigilante ne daya aka kashe, sai aka raunata dan sa kan Community Watch Corp' daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post