Gobara ta tashi a ofishin 'yan sanda a jihar Kano.

An samu tashin gobara a ofishin ‘yan sanda na a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano da sanyin safiyar ranar Litinin dinnan.

 kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel,ya bayyana haka ga manema labarai inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 05.45 na safe inda wani gini daga ciki ya kone gaba daya duk da cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai dauki.

Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar har zuwa wannan lokaci.

Yace an killace yankin domin hana kutsawar bata-gari, domin akwai makamai da alburusai da ke cikin ofishin wannan dalilin yasa aka rufe shige da fice a wajen

A halin yanzu dai Babban  jami’in ‘yan sanda na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa kamar yadda kwamishinan ya fada. 

​An samu tashin gobara a ofishin ‘yan sanda na a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano da sanyin safiyar ranar Litinin dinnan.

 kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel,ya bayyana haka ga manema labarai inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 05.45 na safe inda wani gini daga ciki ya kone gaba daya duk da cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai dauki.

Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar har zuwa wannan lokaci.

Yace an killace yankin domin hana kutsawar bata-gari, domin akwai makamai da alburusai da ke cikin ofishin wannan dalilin yasa aka rufe shige da fice a wajen

A halin yanzu dai Babban  jami’in ‘yan sanda na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa kamar yadda kwamishinan ya fada. 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp