Gwamnatin Tinubu ba ta da alhakin jefa al'ummar Nijeriya cikin matsi Inji Sunusi.

 Gwamnatin Tinubu ba ta da alhakin jefa al'ummar Nijeriya cikin matsi Inji Sunusi. 



Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Muhammed Sunusi, ya ce rashin adalci ne a zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan halin matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki a halin yanzu.


Sunusi ya ce Nijeriya na fama da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon rashin gudanar da manufofin tattalin arziki na shekaru takwas da suka gabata.


Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi  ranar Lahadi a wani taro daya gudana  a Abuja, 


ya ce ba zai bi sahun masu sukar Tinubu kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu ba, Indai za'ai uzuri ba tun yanzu ake fama da wannan matsin ba. 


Sanusi ya ce ya shafe shekaru yana magana a kan matsin da ake ta fama da shi kafin tabarbarewar tattalin arziki. Duk wani masanin tattalin arziki a Nijeriya ya yi nazarin manufofin a cikin shekaru takwas da suka wuce ya san cewa ‘yan Najeriya za su fada cikin wannan mawuyacin hali.


Yace sunsha fadawa al'ummar Nijeriya cewa za'a shiga wannan halin, kuma dole sai anbi manufofin da masana tattalin arziki suka bayyana sannan za'a samu sauki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp