Ki sanar da mijinki halin da 'yan Nijeriya ke ciki, sakon Sarkin Kano ga matar Tinubu.

 Ki sanar da mijinki halin da 'yan Nijeriya ke ciki, sakon Sarkin Kano ga matar Tinubu. 


Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga uwargidan Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ta sanar dashi halin matsi da yan Nijeriya ke ciki. 


Sarkin yayi kiranne yayin wata ziyarar da Remi Tinubu ta kai kano, ya kuma bukaci shugaban kasar da ya gaggauta magance matsalar rashin tsaro a shiyyoyi shida na Nijeriya domin a cewar sa wannan babban kalu balene. 

 

Yace al'ummar kasar nan na cikin mawuyacin hali na matsin rayuwa don haka dole shugabanni su tashi tsaye domin nemowa al'umma mafita. 


Batun rashin tsaro wata babbar matsala ce da gwamnatin Tinubu ta gada amma yakamata gwamnati tayi iyakar kokarinta wajen kwarda matsalar tsaro a fadin kasa. 


Da yake magana kan batun mayar da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN) da wasu ma’aikatun babban bankin Najeriya (CBN) zuwa Legas, Sarkin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta fito da tsari na wayar dakan al'umma ta hanyar da zasu gane domin ta hakane za'a samu fahimta tsakanin gwamnati da al'umma. 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp