Gwamnonin PDP sun bukaci Tinubu ya magance tsadar abinci


 Gwamnonin PDP sun bukaci Tinubu ya magance tsadar abinci da ake fama da ita a dukkanin fadin kasar. 


Gwamnonin sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a karshen taron nasu wanda kuma shugaban kungiyar Gwamna Bala Mohammed ya karanta a Abuja ranar Litinin.

 Mohammed ya ce gwamnonin a taron sun yi nazari kan halin da al’umma ke ciki, wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon kalubalen tattalin arziki da tsaro da al’ummar kasar ke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post