Kaso 30% na jariran da ke mutuwa a duniya 'yan Nijeriya ne inji wani rahotoKwamitin kwamishinonin kiwon lafiya a Arewa maso gabashin Najeriya na bukatar Hukumar Raya Cigaban yanki wato North East Development Commission ta yi hoɓbasa wurin ceto rayukan jarirai da iyayen su da ke mutuwa kafin da kuma bayan haihuwa.

A cewar wannan kwamiti kaso talatin cikin ɗari na mutuwar mata masu juna biyu da jariri a Najeriya ya ke faruwa, saboda haka shugaban wannan kwamiti Farfesa Baba Malam Ganã a wata ganawa da suka yi da hukumar ta NEDC ya ce ya kamata hukumar ta yi dukkan mai yiyuwa wurin taimakawa, dan ganin an magance matsalar. 

Wannan matsala inji Farfesa Ganã tana tayar da hankalin hukumomin kiwon lafiya a Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoto na baya-bayanan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar ya nuna cewa Nijeriya ce ta biyu a irin wannan matsala ta mace-macen mata masu juna biyu da yara ƙanana.

Post a Comment

Previous Post Next Post