Karin bayani kan takunkumin da ECOWAS ta janye wa Nijar

 

Kola Sulaimon / AFP


ECOWAS da shugabanninta sun lashe amansu bayan da a taron kungiyar a Abuja, ta janye wasu daga cikin takunkuman da ita da kanta ta lafta wa Nijar don ladabtar da sojojin da suka hambarar da gwamnatin dimukuradiyya a shekrar da ta gabata. A sanarwar da ECOWAS din ta fitar ta ce a hankali za ta janye sauran, amma ta ce ta janye wa kasashen Mali da Guinea takunkuman kudi da tattalin arziki. Sai dai ‘yan Nijar sun fi damuwa da bukatar a janye musu takunkuman iyakoki da kudade da na wutar lantarki wanda kawo yanzu sanarwar ta ECOWAS ba ta ce komai a kai ba. 





 

Tun bayan lafta wannan takunkumi dai, hukumomin mulkin sojan kasar suka dukufa wajen lalubu hanyoyin rage radadin takunkumin amma kusan ba su yi wani tasiri ba duba da yadda farashin kayayyakin musamman abinci ya ki sauka tare da ci gaba da fuskantar matsalar rashin wadatuwar kudade a hannun mutane.

 

To sai dai duk da wannan yanayi da aka shiga sojojin suka ci gaba da kafewa kai da fata ak an matsayin su har ma a karshe suka ayyana ficewarsu tare da takwarorinsu na Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar baki daya  don haka ne ga masu fashin baki irinsu Dr Gambo Alhaji Sani masanin kimiyar siyasa a Jami'ar André Salifou ta Damagaram ke ganin dole ne kungiyar ta ECOWAS ta rungumi kaddara domin kuwa ta ga ba wurin zuwa ne sai gona shi ya sa ta ci tuwon fashin, mai sharhin ya shaida wa DCL Hausa cewa duk da ECOWAS ta janye takunkuman amma zai wahala idan yanzu sojojin na Nijar za su janye fita daga kungiyar da suka yi domin sun yanka sun ga jinni

Tun farkon wannan mako mai karewa ne dai rahotanni cire takunkumin na ECOWAS kan Nijar ke yawo kafin a tsakiyar makon tsohon shugaban kasar Tarayyar Najeriya Yakubu Gowon wanda ke cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS ya yi kira ga kungiyar  da ta gaggauta cire Nijar din takunkumin da ta kakaba mata.

Post a Comment

Previous Post Next Post