Hukumar Kwastam a Nijeriya ta fara siyar da kayan abinci ga Yan kasar.

 Hukumar hana fasa kwauri a Nijeriya (NCS) ta kaddamar da wani shiri na rage karancin abinci a Najeriya. 

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam (CGC), Bashir Adewale Adeniyi MFR, ya bayyana kudirinsa na ganin ya dace da shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalar karancin abinci ta hanyar tabbatar da wadatar kayan abinci ga ‘yan Nijeriya ana siyar da shinkafar Naira 10,000 akan kowane buhu 25kg.


Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rabon shinkafar a Legas a ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairu, 2024, CGC Adeniyi ya jaddada cewa za a yi rabon shinkafar ne a wuraren da ake gudanar da ayyukan kwastam, tare da tabbatar da samun masu amfana kai tsaye.


 Adeniyi ya jaddada mahimmancin tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin shirin rabon, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da ke shiga wannan shiri da su guji sayar da shinkafar a kasuwanni ko kuma tara ta domin wasu dalilai da ba na cikin gida ba.


Inda ya bayyana cewa hukumar ta kwastam ta samu amincewar gwamnati na bayar da kayayyakin abincin da aka kama ga mabukata a kan farashi mai rahusa bayan ta gamsu da aikin tantance lambar shedar dan kasa ta (NIN).
Post a Comment

Previous Post Next Post