APC na bakin kokarinta don inganta rayuwar al'umma - Bala Abu Musawa

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya ce gwamnatin APc a jihar na bakin kokari nta don ganin ta kyautata tare da inganta rayuwar al'ummar jihar da ke lungu da sako na jihar.

Alhaji Bala Abu Musawa na magana ne a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman don duba ayyukan da ake gudanarwa a lungu da sako na jihar.

Tawagar da Alhaji Bala Abu Musawa ya jagoranta, ta ziyarci illahirin kananan hukumomin da ke shiyyar Daura a jihar su 12.

A duk kananan hukumomin da aka ziyarta, shugabannin kananan hukumomin sun tarbi tawagar sun kuma zagaya da su a kauyukan da ke cikin kowace karamar hukuma domin duba ayyukan da ake gudanarwa na ci gaban al'umma.

Alhaji Bala Abu Musawa ya ce wannan ziyara na da nufin karfafa guiwa ga shugabannin kananan hukumomin na su kara azamar aiwatar da ayyuka ga alummominsu.

Mataimakin shugaban jam'iyyar ta APC ya ce gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda a jihar ba ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin ta samar da saukin rayuwa ga mutanen da ke lungu da sako na jihar.

Shiyyar Daura sai ta kunshi kananan hukumomin Mani, Bindawa, Mashi, Dutsi, Kankia, Kusada, Ingawa, Daura, Sandamu, Mai'adua, Baure da Zango.

Post a Comment

Previous Post Next Post