Bankin CBN ya fito da sauye-sauye masu tsauri ga 'yan chanji


Babban Bankin Najeriya ya sanya wa yan chanji dokar dole sai wanda yake da jarin Naira miliyan 500(tier2) ko biliyan biyu ne za a ba shi lasisin (tier 1)

Karin haske a game da tsarin :
-Mai lasisin 'Tier 1' zai iya mu'amala kai tsaye da CBN kuma za a yi ba shi damar bude rassa wuraren chanji a kowacce jiha a Najeriya.
-Mai lasisin 'Tier 2' kuma sai dai ya yi mu'amala da bankunan kasuwanci kuma a jiha daya kawai zai iya bude wurin chanji kudi amma zai iya yin rassa a wannan jihar.
-A baya mai jarin miliyan 350 yana iya samun 'Tier 1' amma yanzu sai jarinka ya kai Naira miliyan 500 zuwa biliyan 2 za a ba ka.

Post a Comment

Previous Post Next Post