Hisbah ta cafke jarumar TikTok Murja Kunya

 


Hukumar Hisbah a jahar Kano ta kama shahararriyar yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya.

Gidan rediyon Freedom ta ruwaito labarin kama Murja a safiyar yau Talata.

Hakan dai ya biyo bayan farautar Murja tare da wasu ƴan Tiktok biyar da Hukumar Hisbah a Jihar ke yi.

Mutanen da hukumar ke nema sun haɗa da Murja, Abubakar Ibrahim (G-Fresh), Sadiya Haruna, Ashiru Idris (Maiwushirya), Ummee Shakira da Hassan Makeup.

Post a Comment

Previous Post Next Post