Zargin kisan kai ya sa an tsare shugaban karamar hukuma gidan yari a Katsina


Kotun Majistare da ke zamanta a Katsina ta tsare shugaban karamar hukumar Batagarawa Alhaji Bala Garba Tsanni a gidan yari bisa zarginsa da kisa, satar mutum.

Ana zargin shugaban karamar hukumar tare da karin wasu mutane 11 da kisan Dagacin garin Dabaibayawa a cikin karamar hukumar Batagarawa ta jihar, Marigayi Alhaji Dikko Ahmad.

An dai gabatar da su gaban kotu ne karkashin sashe na 59, 249 da 189 na kundin penal code.

Tun da farko dai Alkalin kotun Majistare Abdulkarim A. Umar ya ba da umurni ga 'yan sanda da su gabatar mata da wadanda ake zargi a ranar 25 ga watan Janairun, 2024.

Tsawon watanni 6 dai sauran mutanen 11 ke tsare a gidan yari, a yayin da aka ba da belin shugaban karamar hukumar.

Da suke gabatar da wadanda ake zargi da aikata wannan lamari, 'yan sanda sun ce sun kammala bincike a kan batun.

A haka ne, Alkalin kotun ya umurci da a tsare shugaban karamar hukumar Bala Garba Tsanni a gidan yari har sai ranar 7 ga watan Maris mai zuwa na 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post