Ba haka ake zawarcin shiga jam'iyya ba, Gwamna Abba ya yi wa Ganduje martani

 Ba haka ake zawarcin shiga jam'iyya ba, Gwamna Abba ya yi wa Ganduje martaniGwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf  ya ce ba shi da niyyar ficewa daga jam’iyyar sa ta (NNPP) da ya ci zabe a karkashinta. 


Gwamna Abba ya bayyana hakan ne kwana daya bayan da shugaban jam'iyyar APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bashi goron gayyatar komawa jam'iyyar APC.


Gwamna Abba Kabir, wanda kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin Gwamnan jihar Kano a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu shi ne kadai gwamna a jam’iyyar NNPP a Nijeriya.


A yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ya gudana a  Kano, Ganduje ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir tare da mambobinsa da magoya bayansa na jam’iyyar NNPP da su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa domin tabbatar da ci gaban siyasar jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post