An kama shugaban jam'iyyar PDP da ake zargi da safarar makamai zuwa jihar Zamfara



Jami'an tsaron hadin guiwa sun ce sun yi nasarar kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai ga barayin daji a jihar Zamfara.

An gano cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Aminu Ibrahim shi ne shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Birnin Yero ta karamar hukumar Shinkafin jihar, kamar yadda jaridun Solacebase da PRNigeria suka samu tabbacin zargin daga majiyoyi na soji a Zamfara.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa an kama mutanen ukun a ranar Litinin da ta gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp