Sojoji sun ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su a Katsina


Rundunar Soji a jihar Katsina sun ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su a makon daya gabata a kauyukan Tashar Nagulle da Nahuta a cikin karamar hukumar Batsari.

Bayan ɗauke mutanan ɓarayin sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 60 domin su sake su.

Mutanen da sojojin suka kubutar aƙwai matan aure da maza da ƙananan yara wanda suka bayyana irin halin ƙuncin da suka samu kansu a hannun ƴan ta'addar.

Post a Comment

Previous Post Next Post