Ana hasashen hauhawar farashin masara, shinkafa a Nijeriya

  


Babbar kasuwar musayar kayayyaki a Najeriya, ta yi hasashen hauhawar farashin masara da shinkafa a wannan shekarar ta 2024.

Kasuwar ta yi hasashen hauhawar farashin masara da kashi 25% da kuma karin kashi 40 cikin 100 na farashin shinkafa.

Ana hasashen farashin makamashi zai ragu da kashi 5 cikin 100 a wannan shekarar sannan ya kara raguwa da kashi 0.7 a shekarar 2025. 

Ana sa ran kayayyakin noma za su ragu da kashi 2 cikin 100 duk a wannan shekarar ta 2024 a cewar kasuwar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp