Ɗalibai 8,285 za su zauna a jarabawar WASSCE ta farko da kwanfuta.


Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma ta sanar cewa ɗalibai 8,285 ne a fadin ƙasarnan suka yi rajista domin fara jarrabawar kammala karatun sakandare a wannan shekarar ta 2024.

Ofishin shugaban hukumar na kasa Amos Dangut ne ya sanar da hakan a yau Litinin a wani taron manema labarai, inda ya ce za a gudanar da jarrabawar daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 17 ga watan Fabrairu.

Shugaban ya kara da cewa, kimanin dalibai 3,949 maza ne, wanda ke da kashi 47.66 cikin 100, yayin da 4,336 mata ne, wanda ke da kashi 52.3 cikin 100.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp