Ba mu kulla yarjejeniya da kowa ba gabanin hukuncin kotun koli - Gwamnan Kano Abba

 


Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya musanta cewa ya kulla wata yarjejeniya da fadar shugaban kasa gabanin hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 12 ga watan Janairun 2024.

Bayanin hakan na acikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Tofa ya fitar yau Litinin.

A yayin da yake mayar da martani kan wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, wadda ke nuni da cewa akwai yarjejeniya tsakanin Gwamnan da fadar shugaban kasa a matsayin wani sharadi na samun nasara a shari’a a kotun koli.

Jaridar DCL Hausa ta ruwaito a ranar 20 ga watan Satumba, kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta kori Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP.

Bayan ɗaukaka ƙara a kotun Koli a ranar 12 ga Janairu, ƙotun ta yi watsi da hukuncin da ƙananan kotuna suka yanke na korar gwamnan a bisa kujerar sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp