Ba mu karbi takarda a hukumance daga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ba - ECOWASKungiyar kasashe masu tattalin arziki ta ECOWAS ta ce har yanzu ba ta karbi wata sanarwa ko takarda a hukumance da ke nuna sun fice daga cikin kungiyar.

A cikin wata sanarwa daga sakatariyar kungiyar ta ce kawai abin da ta sani shi ne tana aiki ba gajiyawa wajen maido da kasashen bisa turbar dimokradiyya.

Ta sanar cewa har yanzu kasashen na da matukar amfani a tafiyar da lamurran kungiyar.

A ranar Lahadin nan dai, kasashen uku na Mali, Nijar da Burkina Faso suka sanar cewa sun fice daga kungiyar ta ECOWAS inda suka ce ana musu barazana. Kasashen uku dai na karkashin jagorancin sojoji bayan da suka hambarar da gwamnatin farar hula.

Post a Comment

Previous Post Next Post