Zulum ya umurci ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu a rajistar zuwa aiki.

 Zulum ya umurci  ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu a rajistar zuwa aiki 


Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta  samar da na'urar daukar bayanai ga shugabannin kananan hukumomin jihar. 


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umarci shugabannin kananan hukumomin da su zauna a yankunansu inda ya bukace su da su sanya hannu a rajistar zuwa aiki a kullum domin tabbatar da kasancewarsu a wuraren aikinsu.


Zulum ya ba da umarnin ne a Maiduguri, babban birnin jihar, yayin da ya jagoranci bikin rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomi 27.


Gwamnan ya umurci ma’aikatar kananan hukumomi da ta gaggauta tura na’urorin daukar bayanai na biometric zuwa kananan hukumomin domin shugabanninsu su rika buga babban yatsa a kullum da karfe 8 na safe, na rana, 2 na rana ko kuma karfe 3:30pm.


Ya ce matakin ya zama dole domin duba rashin zuwa aiki ko kuma kauce wa aiki da kowane shugaba ba tare da dalili na gaske ba kamar yadda wasu yi a baya.


Gwamnan ya bayyana cewa yadda ake samun ingantaccen tsaro a fadin jihar, akwai bukatar shugabannin kananan hukumomin su kasance tare da jama’arsu domin tallafa wa kudirin gwamnatinsa na gyara, sake ginawa, da kuma tsugunar da ‘yan gudun hijira a jihar inda

ya bukace su da su sarrafa karancin albarkatun kananan hukumomin bisa adalci da rikon amana.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp