Sojojin sama na bin hukumar zaben INEC bashi a Nijeriya.
Shugaban hafsan sojin saman Nijeriya Air Marshal Hassan Bala Abubakar, ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (INEC) da ta biya wasu basuka da sojojin na sama ke bin ta.
Abubakar Hassan ya yi wannan kiran ne a Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar hukumar ta INEC, karkashin jagorancin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, da suka ziyarci hedikwatar rundunar sojin sama.
Yace ya yi amfani da wannan dama domin tunatar da shugaban INEC cewa akwai kudaden sojojin samar ke bin hukumar INEC da ya kamata a ce an biya.
Kuma biyan wannan kudaden zai ba rundunar ta sojin sama damar, ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin walwala da kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.